Wannan lamarin ya sa gwamnonin arewa suna ganin dole ne a tashi tsaye a ciwo kan ta'adanci.
Gwamnonin sun lashi takobin tallafawa da bukatan al'umma su gudanar da addu'o'i na musamman saboda kawo karshen matsalar dake neman gagarar kundila.
Sanata Muhammad Bindo gwamnan jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da abun ya fi shafa yace zasu gudanar da wani taro na musamman domin hada karfi da gwamnatin tarayya wajen yakar ta'adanci. Amma a matakin farko ya bukaci jama'a su gudanar da addu'o'i. Yace yanzu matsalar ta kai har Kaduna da Kano da Jos. Yana ganin tunda shugaban kasa na yanzu kwararre ne akan harkokin tsaro ya san abun da zai yi.
Dangane da abun da gwamnonin arewa zasu yi gwamnan yace suna shiri amma ba abun da za'a bayyana a bainar jama'a ba ne. Yace a cigaba da addu'a sauran kuma gwamnatoci suna yin nasu.
To saidai kungiyoyi da manazarta na kiran jami'an tsaro da su sauya salo tare da yin anfani da naurorin zamani domin zakulo 'yan ta'ada..Alhaji Aliyu Haman Tukur Ribadu kusa a kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ya bada shawarar cewa a kawo motoci da wasu naurori da zasu gano muggan makamai yayin bincike. Yace harkar tsaro yanzu ta wuce na jami'an tsaro suna lekawa cikin motoci suna bincike. Yace akwai narorin da zasu gano makamai ko bom kafin ma a zo kusa.
Idan ba an yi anfani da kimiya da fasaha ba da wuya a shawo kan 'yan ta'ada ko a ganosu.
Su ma shugabannin addini suna gudanar da addu'o'i akan matsalar ta'adanci. Shugaban kungiyar IZALA Shaikh Abdullahi Bala Lau ya jagoranci addu'a ta musamman akan ta'adanci.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.