Yanzu haka dai kungiyoyin addini a kasashen Africa sun fara mayar da matrtani akan matakin da gwamnatin kasar Chadi ta dauka na haranta sanya nikabi saboda matakan tsaro biyo bayan wani kunar bakin wake da ya hallaka mutane a kasar ta Chadi a cikin makon jiya, kungiyar Izala na cikin kungiyoyin dake waazi a kasashen Africa ta yamma Sheik Sambo Rigacikum shine mataimakin shugaban kungiyar a Najeriya.
‘’Duniya fa yau abinda ake tutiya dashi demokaradiyya sukan mata lakabi da cewa Government of the People By the people for the people, to in demokaradiyya akeyi a duniya dome wasu zasu dauki nikabi ko hijabi suce salo ne na gudanar da addinin su sannan wata gwamnati tace zata hana su in anyi haka ina demokaradiyyar take’’
Ga dai Mustafa Nasir Batsari da Karin bayani