Kungiyar ta raba kayan abincin ne ga wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.
'Yan gudun hijiran fiye da dubu goma sha shida dake zaune tare da mutane a gidajensu a sassa daban daban suka samu tallafin kungiyar. Kungiyar tace ta dauki matakin ne domin rage irin wahalun da mutane suke ciki, musamman wadanda ke rike da 'yan gudun hijiran a gidajensu.
Imam Baba Kure Gwani mataimakin majalisar malamai na kungiyar Izalan yace sun kashe kudi kimanin nera miliyan sittin domin sayen kayan abincin da suka hada da shinkafa, mai da sukari. Kawo yanzu sun yi kwana hudu suna raba kayan abincin musamman a birnin Maiduguri ga wadanda suke rie da 'yan gudun hijiran.
Kungiyar ta zabi ta rabawa masu rike da 'yan gudun hijiran a gidajensu tallafi domin wadanda suke sansanonin 'yan gudun hijira suna samun tallafi daga gwamnati. Gwamnati bata damu da wadanda suke zaune a gidajen mutane ba dalili ke nan aka raba masu tallafi domin su samu sauki.
Wasu da suka anfana da tallafin sun godewa Allah da ita kungiyar Izala da ta kawo masu doki. Tallafin da kungiyar ta bayar ya nunawa jama'a cewa kungiyar ta tsaya daram domin ta taimakesu da kuma jama'ar da ta tagayyara.
Ga karin bayani.