Ingila ta bada sanarwar amincewar huldar Jakadanci/Diflomasiyya ga Majalisar kula da ayyukan jagorancin kasa dake karkashin masu adawa da Gwamnatin shugaba Moammar Gadhafin Libya.
Jin haka ne kuma sai shugabannin majalisar kula da ayyukan jagorancin Libya suka bada sanarwar janye amincewar da tun farko suka yi na kyale Gadhafi ci gaba da zama a Libya idan har ya amince ya ajiye mukaminsa na shugaban Libya.
Jiya laraba Ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague yake cewa Gwamnatin Birtaniya ta bada umarnin korar dukkan jami’an jakadancin kasar Libya daga Birtaniya, sannan ta gayyaci Majalisar mayakan ‘yan tawayen Libya da su tura nasu jami’an da zasu maye gurbin na Gwamnatin Gadhafi.
Yace Birtaniya ta dauki matakin yin haka ne domin karfafa karfin fada ajin hukumar mulkin ‘yan hamayyar Libya a kasa da kasa, kuma hakan ya basu ‘yancin kafa sabuwar halattaciyar Gwamnati a Libya.