Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gwabza Kazamin Fada A Zawiya


'Yan tawayen Libya, cikin motar a-kori-kura, sun doshi bakin daga a kusa da Zawiya, ranar asabar 13 Agusta 2011.
'Yan tawayen Libya, cikin motar a-kori-kura, sun doshi bakin daga a kusa da Zawiya, ranar asabar 13 Agusta 2011.

Dakarun 'yan tawaye da na shugaba Muammar Gaddafi su na gwabza kazamin fada domin neman mallakin wannan gari mai matukar muhimmanci a kusa da Tripoli, babban birnin kasar.

Ana gwabza kazamin fada a tsakanin ‘yan tawaye da askarawa masu yin biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya a garin Zawiya, mai matukar muhimmanci a fagen yaki, kuma mai tazarar kilomita 50 kacal a yamma da Tripoli, babban birnin kasar.

A yau lahadi ‘yan tawaye suka ce sun samu kaiwa har tsakiyar birnin. Amma gwamnatin Libya ta ce har yanzu Zawiya tana nan daram a hannunta. Zawiya tana kan babbar hanyar motar da ta taso daga Tripoli zuwa bakin iyakar Libya da Tunisiya. Idan ‘yan tawaye suka kama garin, zasu tsinke hanyar da birnin Tripoli ke samun kayyakin bukatunsa.

Tun cikin watan Fabrairu mayaka masu adawa da Gaddafi, wadanda ke samun tallafi daga hare-haren da jiragen saman NATO suke kaiwa a kan sojojin gwamnati, suke kokarin kaiwa ga babban birnin a yunkurin tumbuke shugaba Gaddafi daga kan mulki.

Jiya asabar, ‘yan tawayen sun ce sun kwace garin Gharyan mai tazarar kilomita 100 a kudu da Tripoli. Amma daga bisani a jiyan, kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci wani mayakin ‘yan adawa yana fadin cewa sabon fada ya barke a garin a bayanda sojojin Gaddafi suka komo tare da karin sojoji da makamai.

XS
SM
MD
LG