Gwamnatin kasar Guinea ta cafke mutane 38 kan hannun da ake zargin suna da shi a hare-hare har biyu da aka kai kan gidan shugaban kasar Alpha Conde a cikin makon jiya.
Wani jamki’in ma’aikatar shara’a na kasar yace wadcanda aka Kaman sun hada da sojoji 25. ba dai abinda ya sami shugaba Conde a lokacinda aka kai wadanan hare-haren a gidansa ran 19 ga watan Yulin nan da muke ciki.
A farmakin farko, shugaba Conde yace maharani sun bude wuta ne akan dakinsa na barci, sai dai ashe shugaban baya dakin a lokacin. Sa’oi kadan bayan haka ne, aka sake kawo hari na biyu akan gidan.
Tun cikin makon jiya din ma hukumomi suka cafke wasu manyan hafsoshin soja biyu na Guinea din da suka hada da tsohon babban hafsan hafs oshin sojan kasar General Nouhou Thiam.
Gwamnatin kasar Guinea ta cafke mutane 38 kan hannun da ake zargin suna da shi a hare-hare har biyu da aka kai kan gidan shugaban kasar Alpha Conde a cikin makon jiya.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024