Shugaban Zambia Rupiah Banda ya tsai da ran 20 ga watan Satumba a matsayin ranar gudanar da zaben kasa da na kananan hukumomi, kuma zai bukaci tsayawa don yin cikakken wa’adinsa a karo na farko.
Mr. Banda ya soke Majalisar Dokoki da na Zartaswar kasar kamar yadda doka ta tanada, a lokacin da aka bayar da sanarwar shirin sabon zaben.
Day a ke jawabi ga kasar baki daya, Mr. Banda y ace das hi da Mataimakinsa na shugaban kasa za su cigaba da gudanar da ayyukansu a matakin zartaswa kuma harkokin gwamnati za su cigaba da gudana kamar yadda aka saba.
Mr. Banda wanda mamban jam’iyyar Movement for Multiparty Democracy ne, ya yi kira ga dukkannin ‘yan takara das u tabbatar cewa an gudanar da zabukan cikin adalci da kuma inganci.
Shugaban ya dare gadon mulki ne bayan wani zabe na musamman a 2008, bayan mutuwar mutumin day a gada wato Levy Mwanawasa. A lokacin zaben, da kyar dai Mr. Banda ya kayar da abokin karawarsa Michael Satan a jam’iyyar Patriotic Front.