Shugaban kwamitin da Gwamnatin Najeriya ta Kafa domin bada shawara wajen magance cin hanci da rashawa a kasar Farfesa Itsay Sagay, ya ce tun ba ya’u ba akwai yarjejeniya dake tsakanin kasashe renon Ingila,na mika duk wani da ake nema a wata kasa na kungiyar domin fuskantar sharia a wata kasa.
Yace da zaran an samu bukatar na mika wani ko wata babban lauyan Gwamnati zai gabatar da wanna bukata ga wata babban kotu, domin tabbatar da cewa laifin da ake neman wanda ake zargin da aikatawa ya fada hurumin laifukan da aka amince a mika mai laifi ga kasar da ta bukaci hakan.
Ko a wannan makon ma sai da shugaba Muhammadu Buhari, ya godewa kasashen Ingila da Switzerland, dangane da goyon bayan da suke baiwa Najeriya, na ganin cewa an dawo da haramtattun kudaden da wasu ‘yan siyasa da shugabani na baya suka sace zuwa kasashen su abunda kuma ya ce zai taimakawa kasashen wajen inganta dangantakar tsakanin su.
Bukatar neman mika Deprieye Alamieyeseigha, tsohon Gwamnan jahar Bayelsa, yaso a dai dai lokacin da wata tsohowar Minista, a ma’aikatar man fetur, a zamanin mulkin Jonathan, Diezani Allison Madueke, ke fuskatar bincike a kasar Ingila, bisa zargin halarta kudaden haram.