Duk da ya ke wutar lantarki ta na inganta a wurare da dama na Najeriya, wasu jama’a na Jahar Naija, daya daga cikin jahohin da ke samar da wutar lantarki ga Najeriya, na kokawa kan rashin wutar lantarkin.
Mutanen Karamar Hukumar Rijau ta Jahar Naija, na korafin rashin samun wutar lantarki, wanda su k ace ya jefa su cikin nau’ukan kuncin rayuwa, al’amarin da su ka ce na illa ga harkokin tattalin arzikin yankin. Wani mai suna Alhaji Ali Maitaba Sabongarin Rijau ya gaya ma wakilinmu a shiyyar Naija Mustapha Nasiru Batsari cewa abin takaici ne ganin yadda wannan gwamnatin ke ta kokarin samar da wutar lantarki a ko ina a Najeriya in banda garin Rijau. Don haka Alhaji Ali na kira ga wadanda abin ya shafa su dau matakin samar masu da wutar lantarki kamar kowa. Shi ma wani mai suna Alhaji Jamilu Mohammed ya ce matsalar rashin wuta a garin Rijau ta kai intaha. Mallam Jamiu mai gayran waya, wanda shi ma ke garin Rijau y ace karancin wuta na matukar gurgunta sana’arsa.
Saboda wadannan koke-koken ne Mustapha ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na kamfanin samar da wutar lantarki da ke Abuja Alhaji Ahmed Shekarau y ace hukumar samar da wutar lantarkin ta na sane da matsalar ta Rijau kuma ta na daukar matakin gyarawa. Y ace lodi ne ya ma ta yawa.
Mustapha y ace banda matsalar lantarki ma yankin na Rijau na fama da matsalar rashin kyawun hanya.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton: