Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama 'Yan Arewa 486 a Abiya


​Da tsakar daren Litinin ne, hukumomin Jihar Abiya suka kama wasu ‘yan arewacin Najeriya su 486 bisa zargin cewa ‘yan Boko Haram ne.

Ganin cewa wannan ba shine karo farko da hakan ke faruwa, ‘yan rajin kare hakkin bil adama sun fara tsokaci.

Comrade Ahmed Muhammad Bunza, shine shugaban cibiyar Habaka Demokradiyya a Najeriya.

“Babu shakka ‘yan arewa suna wahala sosai, musamman a kudancin Najeriya, saboda a kwanakin baya an kama wasu ‘yan arewa a Legas, sannan an kama wasu a Imo an mayarda su arewa,” a cewar Comrade Bunza.

Mr. Bunza yayi karin haske akan ko matakan da hukumomin kudancin kasar ke dauka, aikin kare kai ne.

“Tun lokacin da abun nan ya fara, an kashe mutane 12,000. Idan aka duba, 9,700, duk mutanen arewa ne. Saboda haka kafin a kashe wani dan kudancin 1, an kashe na arewa 1,500. Maimakon a bar mutanen arewa su ji da abinda ke cinsu a cikin zuciya, sai ake fitoda wasu abubuwa, ana zargin ‘yan arewa da su.”

Comrade Bunza ya karkare da cewa akwai jahilci game da yadda ake gudanar da matakan tsaro a Najeriya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG