Babban kalubale da gwamnatin shugaba Buhari ke fuskanta shi ne ya iske baitulmalin kasar fanko ba komi ciki.
Duk abun da aka sani na arzikin kasar an sace. An bar kasa da talauci.
Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya amma ya shiga wanna matsalar. Amma babu wanda zai warware matsalar kasar sai shi Buharin. Shi ne zai iya fitar da 'yan Najeriya daga mugun matsalar da suka fada ciki.
Matsalar shugaban ita ce ta rashin kudi da kuma yadda aka yi aka shiga rashin kudin saboda an yi sace-sace da yawa an nuna tashin gaskiya.Bugu da kari ba'a bin ka'ida ana ksar kamar yadda ya kamata a yi.
Kowa yana yin abun da ya ga dama ne saboda an samu shugabanni da basu da adalci da kuma tausayawa mutane..Babu abnu da sa ga sai barna da dukiyar kasar yadda suka ga dama.
Batun cewa a binciki shugabannin da suka shude ko kada a bincikesu magana ce mara ma'ana. Idan har ana son a gyara kasa a kuma sake ginata dole ne a hukunta duk wanda ya karya doka koda ya aikata laifin ne shekaru talatin ko arba'in da suka gabata. A Turai ko Amurka kowacce shekara ka yi sai an bincikeka idan har ka yi rashin gaskiya.
Rashin gaskiy ba Buhari ba ne ya kawo dokoki. Ka'idar mulki ce ta tabbatar da dokar rashin gaskiya. Akwai tsarin mulkin kasa da ya hana rashin gaskiya. Saboda haka kowanene ya aikata rashin gaskiya a hukumtashi.
Idan har ana son a gyara kasa ba za'a bar wadanda suka aikata rashin gaskiya ba domin ba'a gina kasa da rashin gaskiya a kasa.
Gaskiya an yi barna da dama amma ba Buhari ne zai fara ba daga koina. Akwai dokoki. Buhari ya ci gaba da aikinsa ya bar dokoki su yi aikinsu. Ya bar irinsu EFCC su yi aikinsu saboda ya kyautatawa jama'ar kasa.
Ba za'a iya yin canji ba kana a bar wasu da suka yi sata 'ya'yan wanda basu yi sata ba su zama bayin 'ya'yan wadanda suka yi sata. Ba'a gina kasa a kan hakan. Saboda haka kada a bar kowane shugaba ne idan dai an sameshi da sata idan za'a yi adalci..
Ga karin bayani.