Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Nemi Bayyani Kan Karkata Basukan da Kasar Ta Ciwo daga Kasashen Waje


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Jiya Shugaba Buhari ya bukaci ma'aikatar kudin Najeriya ta bayyana masa yadda aka karkata basukan da kasar ta ciwo daga kasashen waje da sunan inganta jiragen kasa

Shugaban Najeriya na son ma'aikatar kudin kasar ta bashi cikakken bayyanin dalilan da suka sa aka karkata basukan da kasar ta ciwo daga kasashen waje da sunan inganta sufuri da jiragen kasa zuwa wasu manufofi daban.

Bayan ya saurari gabatarwar ma'aikatar sufuri daga bakin babban sakatarenta Alhaji Muhammad Bashar a fadarsa ta Aso Villa shugaba Buhari yace abun takaici ne a ce an yi anfani da basukan da aka ciwo daga kasashen waje ba akan dalilana da aka karbosu ba tare da kin bin yarjejeniyar da aka shata.

Shugaban yace ta yaya za'a ce an ki bin manufofinda aka bayar kafin a bada bashin kana a zagaya a yi anfani da kudin kan wasu manufofi daban.

Shugaban yace "ina fata an bi ka'ida kafin a karkata basukan. Fidda kudi daga wani aikin da aka karbi kudin saboda dashi zuwa wani daban to dole ne a yi hakan akan kai'da"

Shugaban yana magana ne musamman akan bashin dalar Amurka fiye da miliyan dubu daya da kasar ta ciwo daga Exim Bank na kasar China da sunan gina sabon layin dogo irin na zamani daga Legas zuwa Kano.

Tun farko sakataren ma'aikatar sufuri wato Alhaji Mumahhad Bashar ya shaidawa shugaban Buhari cewa dalar Amurka miliyan dari hudu ce yanzu ta rage tare da ma'aikatar kudi. To ko ina dala miliyan dari shida ta shiga?

Shugaba Buhari ya nuna bakin ciki akan yadda shekara da shekaru gwamnati ta kan kasa bada nata kasonidan ta karbo kudi daga waje saboda yin wani aiki na mausamman. Rashin bada nata kason ne ya kan kaiga barin aikin ba tare da kammalashi ba. Sai kasar tayi biyu babu, wato babu kudin babu aikin..

Shugaba Buhari yace yanzu a fili take cewa dole ne a sake daidaita ayyukan ma'aikatar sufuri tare tsarasu daga wanda ya fi mahimmanci har zuwa wanda za'a yi a baya.

Daga bisani babban sakataren ma'aikatar sufufri Alhaji Muhammad Bashar ya bayyanawa shugaban irin kalubalen da ma'aikatar ke fuskanta. Wadan nan kuwa sun hada da yadda mutane ke mamaye filayen jiragen kasa, da rashin tsaro akan hanyoyin jiragen ruwa da yarjejeniya tsakanin hukumar tasoshin jiragen ruwa da kamfanonin dake kula da tsoshin wadda take cike da rudani.

XS
SM
MD
LG