Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kula Da Alhazai A Najeriya Ta Yi Karin Haske Kan Aikin Hajjin Badi


NAHCON
NAHCON

Biyo bayan dakatar da damar zuwa hajji shekaru biyu a jere da Saudiyya ta yi don kalubalen coronavirus, hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta tara dukkan jami'an labarun hukumomin alhazai na jihohi don bitar halin da ake ciki.

NAHCON ta ce ya zama wajibi a samu bayanai na bai daya ga maniyyata don ba su kwarin gwiwar cewa da yardar Allah za a cimma burin sauke faralin.

Shugaban hukumar Zikrullah Kunle Hassan ya ce duk da rashin zuwa hajjin, hukumar na ci gaba da tsare-tsare kan yadda za a tunkari zuwa hajjin da zarar an bude dama don amfanin dubban maniyyata daga Najeriya.

Kunle Hassan wanda a shekarar da ya hau mukamin jagorancin hukumar duniya ta fada kalubalen coronavirus, ya ce wajibi ne hukumar ta rika samar da bayanai ga maniyata don zama cikin shirin gujewa fafe gora ranar tafiya.

Mahalarta taron sun bayyana irin tambayoyin da suke samu daga maniyyata kan aikin hajjin da yake cikin runkunan Musulunci biyar.

NAHCON
NAHCON

Karin bayani akan: Dr. Aliyu Tanko, NAHCON, Saudiyya, Nigeria, da Najeriya.

A gefe guda hukumar ta na kara inganta shirin adanar kudi don samun gudanar da aikin hajji ta hanyar ajiyar kudi na tsawon lokacin da maniyyaci zai iya tara kudin kujera.

Kamar yadda shugaban sashen Dr. Aliyu Tanko ya fada, tsarin tamkar wanda a ke yi ne a Malaysia inda mai niyya zai yi ta tara kudi har ya samu damar akalla ya je hajji a rayuwarsa sau daya.

NAHCON da a ka kafa a 2006 daga sashe a ma'aikatar waje, kan zama mai shiga yarjejeniya a madadin jihohi kan aikin hajji da Saudiyya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hauwa Umar:

Hukumar Kula Da Alhazai A Najeriya Ta Yi Karin Haske Kan Aikin Hajjin Badi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina

Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00


XS
SM
MD
LG