Taron majalisar ministocin da ya gudana a yammacin jiya alhamis a karkashin jagorancin shugaban kasa Mohamed Bazoum ne ya bada tabbaci dangane da arangamar da aka yi a tsakanin ‘yan bindigar da suka datse hanya da a daya bangaren tawagar jama’ar Banibangou mai kunshe da mutane 84.
Lamarin wanda ya wakana a wani wurin dake kimanin kilomita11 da kauyen Adabdab dake a tazarar km 50 a arewa maso yammacin Banibangou ya yi sanadin mutuwar mutane 69 cikinsu har da magajin garin Banibangou yayinda wasu 15 suka tsira da rayuwarsu inji sanarwar gwamnatin ta Nijer dake zuwa kwankin 2 bayan faruwar wannan al’amari.
Domin nuna alhinin wannan babban ta’adi hukumomi sun ayyana zaman makokin kwanaki 2 a dukkan fadin kasar ta Nijer daga yau juma’a yayinda suka ce sun barbaza jami’an tsaro domin farautar masu hannu a wannan aika aika. Suna masu cewa gwamnati za ta ci gaba da saka kafar wando 1 da ‘yan ta kife yayinda aka gargadi jama’a da yin takatsatsan.
Koda yake hukumomi na kiran mutanen da wannan hari ya rutsa da su a matsayin tawagar magajin gari masu bin diddigin masana irinsu Alkassoum Abdourahaman na cewa mayakan sa kai ne suka fada wannan tarko a daidai lokacin da suke aikin sintiri don kare jama’arsu daga barazanar ‘yan ta’addan da ke tsallowa daga Mali .
Kisan magajin garin Banibangou da wasu gwamman matasan gundumarsa wani abu ne da ya sake farfado da mahawara a game da halin da ake ciki a jihar Tilabery musamman a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta inda wasu ke tunatarwa akan bukatar nada jami’an tsaro don shugabancin a daukacin kananan hukumomin jihar a maimakon ‘yan siyasa fararen hula duk da irin dimbin matakan tsaro da gwamnati ta dauka yayinda wasu ke ganin ba a nan hgzo ke sakar ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: