A washe garin harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar jandarmomi 19 a ranar 31 ga watan yulin da ya gabata a karkarar Torodi dake jihar Tilabery ne sojojin jamhuriyar Nijer suka kaddamar da wata rawar daji mai sunan BILLOUGOL de Boni da nufin zakulo masu hannu a wannan mummunar ta’asa lamarin da ya bada damar hallaka ‘yan ta’adda a kalla 100 hukumomi sun yaba da samun wannan galaba dake zama abin alfahari.
Haka-za-lika a yayin wannan samame askarawan na Nijer sun lalata motoci da dimbin harsasai da ma’ajiyar man fetur a wannan yanki dake tsakiyar iyakar Nijer da Burkina Faso da fadamar kogin Sirba.
Wani dan rajin kare hakkin jama’a Son Allah Dambaji na cewa irin wannan nasara abu ne da ka iya kwantar da hankalin talakawa musamman mazauna yankunan da ake fama da matsalar tsaro.
Samun goyon baya daga jama’a da tanadin wadatatun kayan aiki tare da karfafa hanyoyin inganta rayuwar jami’an tsaro daga bangaren mahukunta abubuwa ne da ya kamata a kula da su don ganin an kai karshen wannan yaki da ya ki ya ki cinyewa a kasashen Sahel inji Hamidou Sidi Fody na kungiyar CODDAE.
A wani labarin na daban wasu mutanen da ake hasashen ‘yan BH ne sun kai hari a garin Baroua na jihar Diffa a cikin daren jiya talata inda suka sace wani mutun sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar murkushe wannan hari tare da karkashe dayawa daga cikin maharan koda yake sojan 2 sun kwanta dama sakamakon wannan gumurzu.
Kawo yanzu babu wata sanarwar hukuma game da wannan al’amari dake wakana watanni 2 kacal bayan da mazaunan Baroua suka koma gida daga sansanin da suka shafe shekaru 6 suna hijira.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: