Rahotanni daga karkarar ta Banibangou sun ce a yayinda suka furtimi wasu ‘yan bindigar da suka kai farmaki a garin Banibangou a yammacin talata ne masu aikin sa kai dake kan babura kimanin 40 suka fada tarkon maharan wadanda suka yi awon gaba da ayarin baraden, cikinsu har da magajin gari kafin daga bisani ya bayyana shi da wasu mutanensa.
Wannan shine karo na 2 da ‘yan bindiga ke afkawa ayarin hukumomi akan hanyarsu ta zuwa wani wuri a jihar Tilabery domin ko a tsakiyar watan jiya shugaban karamar hukumar Bankilare ya ketare rijiya da bayba akan hanyarsa ta komawa gida daga garin Ayorou abinda ke kara fayyace aniyar ‘yan ta’adda a wannan yanki.
Kawo yanzu ba wani martani daga bangaren hukumomi dangane da wannan al’amari dake faruwa makwanni 2 bayan da majalisar dokokin kasa ta baiwa gwamnatin Nijer izinin tsawaita dokar ta baci a mafi yawancin gundumomin jihar Tilabery cikinsu har da gundumar Banibangou wace al’umarta ta bijirewa dokar hana zurga-zurgar babura duk da cewa ita ce karkarar da ake dauka a matsi wace tafi ko ina hadari a jihar ta Tilabery saboda kusancinta da yankin da ‘yan ta’addan Mali ke da sansani.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: