Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Farfado Da Tsarin Gudunmawa Ta Ciyar Da Yara A Makarantun Boko

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko
Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko

Hukumomin Nijar sun gudanar da wani taron hadin gwiwa da jakadun MDD  da na kungiyar EU da nufin jan ra’ayin masu hannu da shuni akan bukatar samun gudunmowarsu  a yunkurin tsarin ciyar da yara a makarantun boko.

NIAMEY, NIGER - Hukumomin kasar na ganin wannan matsayin wani bangare na matakan inganta sha’anin ilimi a yankunan da har yanzu jama’a ke dari-dari da sha’anin boko.

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko
Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko

Ciyar da yara a makarantun boko da ake kira Cantine Scolaire wani tsari ne da aka yi amannar cewa ya na taimakawa wajen bunkasa sha’anin ilimi sakamakon yadda matakin ke kara wa iyaye kwarin gwiwar tura ‘ya'yansu makaranta yayin da abin ke cusa wa yara kwadayin zuwa aji.

La’akari da hakan ne ya sa gwamnatin kasar ta fara yunkurin fadada wannan tsari da tuni ya haifar da kyakkyawan sakamako a kasashe makwabta mafarin shirya wannan haduwa don neman gudunmowar masu hannu da shuni kenan.

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko
Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko

Hukumar abinci ta duniya WFP kokuma PAM wacce ke tallafa wa Nijar a tsarin wucin gadin ciyar da yara abinci a makaranta, ta jaddada aniyar ci gaba da bada gudunmowa, inji wakilin hukumar Jean NOEL Gentile.

Ya ce hukumar PAM na nan kan bakarta a wannan aiki na hadin gwiwa da gwamnatin Nijar. Aiki ne da ke bukatar a samu karin kudade daga abokan hulda masu hannu da shuni haka kuma abin na bukatar gwamnati ta ware wani kaso daga kasafin kudade a nan gaba domin al’ummomin da muke tallafa wa da abubuwan inganta yanayin rayuwarsu kamar su ayyukan samar da abinci da kudaden shiga ta yadda wata rana su da kansu zasu iya ba da gudunmowa a ayyukan ba yara abinci a makaranta.

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko
Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko

Sarakunan gargajiya sun sha alwashin ganar da talakawa akan mahimmancin wannan tsari a matsayinsu na shugabanin al’umma, inji Sarkin Sakoira Honorable Dr. Moussa Sadou Kalilou.

Mai martaba sarkin na cewa aikinmu ne wannan za mu fadakar da al’umma don ganin kowa ya bada gudunmowar da za ta taimaka wa dorewar wannan tsari na ciyar da yara a makaranta.

Saurari cikakken rahoton daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Wani Taron Gudunmawa Na Ciyar Da Yara A Makarantun Boko.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG