BIRNIN N’KONNI, NIGER - Kasancewa maganar tsarin iyali na ci gaba da haifar da mahawarori masu zafin gaske a Jamhuriyar Nijar tsakanin malaman addini da hukumomin kasar ya sa kungiyar ta yi hada wannan taron.
Musulman da kiristoci sun ce sun amince da tsarin iyali, amma sun yi fatali da maganar kayyade iyali.
Biyo bayan zafin da al'amura suka yi a Jamhuriyar Nijar a 'yan watannin da suka gabata da a can shekarun baya tsakanin malaman addini da hukumomin kasar game da maganar tsarin iyali, shi ya sa kungiyar nan mai kula da hada kan mambobin addinai CDIR ta hada malaman addinai na Musulmai da Kiristoci game da maganar saka sarari tsakanin haihuwa.
Taron ya wakana a garin birni N'Konni, ya sa ma malaman addinan yin kai guda, game da amincewa da maganar tsarin iyali ko da yake sun yi watsi da maganar kayyade iyali.
Kasancewa, ana yawan samun sabani game da maganar ta tsarin iyalai tsakanin hukumomin kasar da malaman addinan, ya sa hukumomin ke ci gaba da bambanta zare da abawa a kan wannan zancan, kamar yanda mai kula da sha'anin sadarwa a hukumar assibitin birni N'Konni Assumane Abdulmumuni ya bayyana.
Maganar tafi shafar ‘ya’ya mata, akan haka ne wata malamar assibiti, tayi bayanin cewa muhimancin tsarin iyali ya kan ‘ya ‘ya mata.
Hukumomi a Nijar, na ci gaba da kira ga ‘yan kasar, da su rungumin tsarin iyali ta la'akari da yadda al'ummar kasar ke karuwa cikin karamin lokaci, ko da yake, abin kan sa suyi hannun riga da malaman kasar, inda abin ke haifar da jijiyoyin wuya a mafi yawacin lokuta.
Saurari cikakken rahoto daga Haruna Mamane Bako: