Jami’an hukumar kula da ‘yan Najeriya da ke ketare (NIDCOM) ta Jordan wacce ke kula da kasar Iraki sun shiga tsakani wajen dawo da wata matashiya mai shekaru 28, Eniola Isaac, wacce aka yi fataucinta zuwa gida.
Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto da aka fitar a Larabar da ta gabata ya bayyana cewa an yaudari Eniola Isaac da alkawarin bogi na samun ingantacciyar rayuwa.
Sai dai, bayan da wadanda suka dauke ta aiki suka jefa ta cikin nau’ukan cin zarafi daban-daban, da duka da takurawa, ta nemi agajin hukumomin Najeriya su taimaka mata ta dawo gida.
A karin bayyanin da hukumar kula da ‘yan Najeriya da ke ketaren ta wallafa a shafinta na X a jiya Alhamis, halin da Eniola Isaac ta tsinci kanta a ciki ya kara bayyana mummunar karuwar da safarar ‘yan Najeriya zuwa kasar Iraki ta hanyar alkawuran karya ya yi.
Dandalin Mu Tattauna