Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya Ta Tasa Keyar ‘Yan Najeriya 7, Da Wasu Zuwa Gida


'Yan Najeriya da aka taso keyarsu
'Yan Najeriya da aka taso keyarsu

An tasa keyar mutanen ne saboda karya dokokin kasar Libya

Hukumar dake yaki da kaura ta barauniyar hanya, wacce kuma ke kokarin ceton bakin haure (DCIM) ta tasa keyar ‘yan najeriya 7, da ‘yan Bangladesh 3 da ‘yan Ghana 3 da ada ake tsare dasu a cibiyar tsare bakin haure ta Qanfoudah zuwa gida.

An taso keyar tasu ne saboda karya dokokin Libya.

Sanarwar da hukumar ta DCIM ta wallafa a shafinta na X a jiya Talata, tace an fidda mutanen daga Libya ne ta filin jirgin saman kasa da kasa na Benina dake Benghazi.

An ruwaito sanarwar na cewar, “DCIM ta tasa keyar bakin haure 13 zuwa kasashensu (‘yan Bangladesh 3 da ‘yan Ghana 3 da kuma ‘yan Najeriya 7) daga cibiyar tsare bakin haure ta Qanfoudah ta filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Benina dake Benghazi. An tasa keyar mutanen ne saboda karya dokokin kasar Libya.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG