Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Yi Kashedi A Kan Ambaliya A Kano Da Makwabtanta


Gidajen sun niste cikin ruwan ambaliya
Gidajen sun niste cikin ruwan ambaliya

Hukumar hukumar kula da yanayi ta Najeriya da ta kula da ayyukan bada agajin gaggawa suna fadakar da al’umar kasar game da matakan kaucewa ambaliyar ruwa.

Itama hukumar kula da koramun Hadejia da Jama’are ta ce ta yi tsare tsaren kubutar da gonakin manoma daga wannan annoba a yankunan jihohin Kano, Jigawa da kuma Bauchi.

Wani rahoto da hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta fitar a makon jiya, ya yi hasashen cewa, jumlar kananan hukumomi 102 ne daga cikin 774 na kasar, ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a damanar bana.

Rahoton ya nuna a jihar Kano, kananan hukumomi 17 ne cikin 44 na jihar zasu iya fuskantar ambaliyar.

Kadan daga ciki sune Gwarzo, Kura, Warawa Wudil , Rinmingado Nasarawa da kuma Kumbotso.

Dr. Kabiru Ibrahim Getso dake zaman kwamishinan muhalli na jihar Kano ya ce rahotan na hukumar kula da yanayi ta Najeriya ya zaburar dasu wajen daukar matakan da suka dace.

Baya ga barazanar rusa muhalli, ambaliyar na lalata amfanin gona na biliyoyin naira a kowace shekara, al’amarin dake jefa manoma halin ni’yasu.

To amma hukumar kula da kogunan Hadejia da Jama’are mai hurumi a sassan jihohin Kano Jigawa da kuma Bauchi, ta ce ta dauki matakan da suka kamata domin kubutar da manoman dake karkashin kulawar ta.

Dinbin manoma ne dai ke tafka hasasara a kowace shekara sanadiyar ambaliyar ruwa yayin da adadi mai yawa na gine-gine ke rushewa a karkara da biranen Najeriya a kowace shekara.

Ga dai rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG