Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ya Sami Shugaban NDDC?


Shugaban NDDC lokacin da ya suma
Shugaban NDDC lokacin da ya suma

Shugaban hukumar raya yankin Neja Delta ta NDDC a Najeriya ya shiga wani yanayi da ake ganin kamar suma ya yi a daidai lokacin da yake fuskantar wani kwamiti da ke binciken almubazarrancin da ake zargin hukumarsa da yi.

Yau ce rana ta hudu na zaman da kwamitin na mambobin majalisar wakilai ke yi yayin da take bincike kan wasu kudaden hukumar.

An shafe kusan sa'a daya ana yi wa Prof. Kemembradikumo Pondei tambayoyi kafin daga bisani aka fahimci cewa ba ya cikin hayyacinsa a kujerar da yake zane kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito.

Wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda Prof. Pondie sanye da wata riga mai launin shudi da ratsin fari ya tintsire ta gefen hannunsa na hagun yayin da yake gaban kwamitin.

Mutane na hango shi suka zo cikin gaggawa domin taimakonsa, lamarin da ya janyo hatsaniya a zauren majalisar.

A cikin faifan bidiyon da ke ta yawo, an ga yadda wani mutum ya yi kokarin bude bakin Pondei yayin da wasu suka yi kokarin fitar da shi.

Mutane na zargin cewa mutuwar bangaren jiki ce da ake kira "stroke" ta same shi. An dai fitar da shi daga dakin taron yayin da kwamitin ya dauki hutun sa'o'i kadan.

Yanzu dai kwamitin ya ci gaba da zaman da yake yi bayan zuwa hutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG