Kafofin yada labarai na Jamus sun ce jami’an Yan sanda na neman mutumin dan kasar Tunisia sakamakon Takardun da aka samu a Motar.
Yan sandan Na Berlin sun samu bayanai kusan 500 daga wayar tarho tun daga lokacin da al’amarin ya faru a ranar Litinin.
Kungiyar Da’esh tayi ikirarin cewa, harin ya biyo bayan kiran da tayi ne ga jama'a da su kaiwa fararen hula hari a kasashen da suke cikin kungiyar hadin gwuiwar da Amurka ke jagoranta da nufin murkushe kungiyar Yan Ta’adda.
Kasar Jamus bata cikin kasashen da suka aiwatar da hare haren jiragen sama akan Yan Kungiyar ta DA’esh a Iraqi da kuma Syria, Amma tana taimakawa da ya hada da Kara Mai a ababawan hawa da kuma Lalubo inda Yan kungiyar ta Da’esh suke.