Mojalli na daya daga cikin ‘yanjaridu shidda da aka kashe a kasar ta Yamen, abinda yassa Yemen din, tareda Iraq, suka zo a matsayi na biyu na kasashen da aka fi asaran rayukkan ‘yanjaridu a bana, a cewar wani rahoto da Kungiyar kare Hakokin ‘Yanjaridu ta Duniya ta sako.
Duka-duka jimillar ‘yanjaridu 48 suka rasa rayukkansu a bakin aiki a wannan shekarar ta 2016, galibinsu a kasashen Syria, Iraq, Yemen, Libya da Afghanistan.
Sai dai kuma duk da yawansu, basu kai yawan wadanda aka hallaka a shekarar da ta gabata ba ta 2015 ba, lokacinda aka kashe ‘yanjaridu 72.
A nahiyar Afrika, jimillar ‘yanjaridu 6 aka kashe, wasu 41 na tsare a gidajen kurkuku daban-daban.
A tsakanin kasashen na Afrika, ba inda aka yi wa manema labarai lahani kamar Somalia inda aka kashe guda ukku a wannan shekarar.