Kotun kolin kasar ta umarci hukumar zaben kasar da ta goge sunayen duk wanda yayi amfani da katin inshorar kiwon lafiya wajen rajista. Kotun dai ta yanke hukuncin cewa katin lafiya bashi da ingancin da za a iya anfani dashi domin yin rajistar jefa kuri'a.
Hukumar zaben, wacce ta fitar da kundin sunayen masu jefa kuri'a, ta fitar da sanarwar cewa duk wanda aka goge sunansa zai iya sake rajistar katin zaben, daga yau juma’a 5 ga wata zuwa juma’a mai zuwa ranar 12 ga wannan wata. An kuma ware ranar da za a yi rijistar mutanen da basu taba yin rijistar zabe ba cikin wannan wata.
Mai magana da yawun hukumar zaben, Eric Dzakpasu, ya fadawa Muryar Amurka cewa kusan sunaye 57,000 ne aka goge daga cikin sunayen mutanen da suka yi rijistar. Har ya zuwa yanzu, ‘kasa rabin mutanen da wannan abu ya sha ne suka sami damar sake yin rijistar. Eric yace hukumar na fatan sama da mutane 32,000 zasu sake yin rijistar.