Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER: Taron Manema Labarai Da Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Kan Masu Zuwa Ci Rani Ta Baruniyar Hanya


tourism in Iran's desert, گردشگری در کویر مرنجاب ایران
tourism in Iran's desert, گردشگری در کویر مرنجاب ایران

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da bakin haure da ‘yan ci rani O.E.M reshen Nijar ta kaddamar da taron manema labarai na kasashen Senegal,da Nijer da Najeriya bisa la’akari da yadda wadannan kasashe suka zama tudun mun tsira ga ‘yan Afirka dake kokarin ketarawa zuwa turai ta barauniyar hanya.

Kara kusantowar ‘yan jarida a yaki da wannan dabi’a domin mayar da hankali wajan wayar da kan jama’a babban matakine da zai taimaka wajan rage wannan matsala dake sanadiyyar rayukan jama’a da dama masu tafiya cirani ta Hamada ko Teku.

Baya ga wayar da kawunan talakawa akan muhimmancin dogaro da kai ta hanyar ayyuka da sana’o’i a nan cikin gida Afirka, wani abinda mahalarta taron ke fatan mayar da hankali akansa, shine jan hakulan shugabannin kasashe kan maganar inganta rayuwar jama’a.

Wata ‘yar jarida daga kasar Senegal ta bayyana cewa taron ya koyar dasu abubuwa da dama akan batutuwan da suka shafi matsalolin ‘yan ci rani, ta dalilin haka ne ta gargadi ‘yan jarida da yin taka tsantsan wajan bada alkaluma dake ban hannu dana hukuma.

Gwamnatin Nijar ta bayyana cewa bayanan data harhado har zuwa ranar 31, ga watan Maris daya gabata, kimanin mutane dubu dari shidda da talatinne ‘yan kasashen yammacin Afirka suka ratsa ta kasar zuwa kasashen turai ta barauniyar hanya.

Jamhuriyar Nijar ta kasance kasa da jama’ar ta ke zuwa ci rani, kuma tana a matsayin kasar da ratsawa ta cikinta ya zama tilasa ga ‘yan yammacin Afirka wadanda suke zuwa cirani kasashen turai ta barauniyar hanya, kuma sau tari take karbar ‘yan ci ranin da aka taso keyar su daga turai.

Ga rahoton Sule Mummini Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG