'Yan adawa sun ce idan sun shiga gwamnati da wa za'a bar talakawa saboda su suka zabi shugaban gwamnati da wadanda suke gwamnati da kuma 'yan adawa domin su kare talakawan.
'Yan adawa su ne suke da bakin magana, su kare muradun talakawa ba su shiga gwamnati ba domin su rasa bakinsu. Su a jam'iyyar MNSD mai adawa sun fadawa shugaban kasar Mahammadou Issoufou ya kai tayin kasuwa.
Tayin da shugaban yayi can baya a wa'adin milkinsa na faro ya yi sanadiyar barkewar baraka a jam'iyyar ta MNSD har wasu manya manyanta suka shiga gwamnati kuma har yanzu ana damawa dasu.
'Yan adawan sun ce duk wanda ya gaji da adawa sai ya rubuto wasikarsa cewa ya bar adawa ko ya fice daga jam'iyyar.
Ga rahoton Souley Moumouni Barma da karin bayani.