Lungu wanda dan jamiyya mai mulkin kasar ta Patriotic Front ne, yace ya samu bayanan sirri dake cewa babbar jamiyyar adawa ta UNITED PARTY FOR NATIONAL DEVELOPMENT ta shirya tada zaune tsaye mudddin bata yi nasara ba wajen zaben.
Sai dai a hirar sa da wannan gidan radiyon Mr Canisius Banda wanda shine mataimakin shugaban jamiyyar ta UPND, yayi kaico da wannan kalamai na shugaba Lungu kuma yace abinda dana sani ne.
Banda yace shugaba Lungu yana da goyon bayan dokar kasa na ganin ci gaba da hada kan kasar, amma yace zai yi anfani da doka mai tsanani, wannan yana kokarin jefa kasar ce cikin halin damuwa, da tashin hankali wanda kuma bai dace ba.
Yace wadannan kalamai na Lungu sun kauce wa hanya, batun cewa zaiyi anfani da doka mai tsanani ma bata taso ba, domin kuwa akwai kwanciyar hankali a kasar bakin gwargwadon hali, Lungu yayi kokari ya mutunta dokar kasar da yayi rantsuwar karewa lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar inji Banda.