Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kare Matakin Ta Na Mayar Da Janal Ahmadu Mohammed Bakin Aiki


Dakarun sojin Najeriya da aka tura jihar Adamawa ke nan a cigaba da dokar ta baci,cikin shirin ko ta kwana.Suna kan hanyarsu ta zuwa kan iyaka,bayan da aka tarbe su a Yola. Hoto Ibrahim Abdul'Aziz.
Dakarun sojin Najeriya da aka tura jihar Adamawa ke nan a cigaba da dokar ta baci,cikin shirin ko ta kwana.Suna kan hanyarsu ta zuwa kan iyaka,bayan da aka tarbe su a Yola. Hoto Ibrahim Abdul'Aziz.

Rundunar sojin Najeriya ta kare matakin da ta dauka na sake maida tsohon kwamandan yaki da Boko Haram, Janar Ahmadu Mohammed bakin aiki bayan da kungiyar rajin kare ‘yan cin Bil Adama ta Amnesty International ta zargeshi da karkashe fararen hula a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ita dai kungiyar Amnesty International, na zargin rundunar sojan Najeriya da sake mayar da tsohon babban kwamandan runduna ta 7 na sojan Najeriya dake Maiduguri, Major Janal Ahmadu Mohammed bakin aiki, bayan da akayi masa ritayar dole a shekara ta 2014.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojan ta fitar, tace anyi wa Janal Mohammed ritayar dole ne ba bisa ka’ida ko la’akari da dokokin soji ba, abin ke nan da yasa bayan ya gabatar da kukansa a hukumance ga majalisar soja, aka duba a tsanake daga baya kuma aka sake mayar da shi bakin aiki.

Kakakin rundunar sojan Najeriya Kanal Kuka Sheka ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Hassana Maina Kaina, cewa an dawo dashi baikin aiki, amma yadda kungiyar ta dauka ba haka abin yake ba, domin lokacin da aka sallameshi ba a bi ka’idar yadda yakamata ba.

Shi kuma kwararre kan aikin soja kuma tsohon gwamnan mulkin soja a jihohin Kano da Benue, Kanal Aminu Isa Kwantagora, yace kungiyar Amnesty International tayi gaggawar fitar da sanarwa akan wannan al’amari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG