Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NEMA Ta Bayyana Yawan Mutanen Da Suka Mutu a Harin Garin Mubi


Yayin da alkaluman mutanen da suka mutu a tagwayen harin kunar bakin wake da aka kai garin Mubi ke karuwa, yanzu haka an garzaya da wadanda ke da munanan raunuka zuwa cibiyar lafiya dake fadar jihar wato FMC Yola.

Alkaluman da hukumar bada agajin gaggawa ta bada a yau Laraba, hukumar ta ce adadin wadanda suka mutu a wannan tagwayen harin kunar bakin wanken sun karu zuwa mutum 30, baya ga wadanda aka garzaya da su zuwa cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya, wato FMC Yola.

Imam Abbani Garki, dake zama jami’in hukumar ta NEMA, mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana halin da ake ciki tare da karyata rahotannin da wasu kafofin yada labarai suka bada dake cewa fiye da mutum 60 ne suka mutu.

Ya zuwa yanzu dai tuni gwamnan jihar Adamawan Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya kira wani taron gaggawa kan harkar tsaro domin gano bakin zaren magance irin wannan tashin hankali.

Ahmad Sajo shine kwamishinan yada labaran jihar Adamawa, ya ce kawo yanzu ba wata kungiya data dau alhakin wannan hari na garin Mubi, yayin da mazauna garin ke danganata shi da irin hare haren da yan kungiyar Boko Haram suka sha kaiwa a baya.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG