Babban hafsan sojojin Najeriya dake kula da aiakace aikace Manjo Janar David Ahmadu ya bayyana wani sabon farmaki da zasu fara kaiwa kan 'yan Boko Haram a arewacin jihar Borno mai taken "Operation Last Hold"
Sabon farmakin ya zama wajibi ne saboda yadda aika aikar kungiyar ta'addancin ya dauki wani sabon salo. Tuni sojojin suka girke manyan kayan yaki tare da sojojin kundunbala. Manufar sabon matakin shi ne a samu a rugurguza kungiyar gaba daya a zirin yankin tafkin Chadi, kamar yadda rundunar mayakan Najeriya tayi bayani.
Wannan sabon farmakin za'a dauki watanni hudu ana yin sa domin a kakkabe 'yan kungiyar ta'addancin a yankin tafkin Chadi, kamar yadda Manjo Janar David Ahmadu ya fada.
Da yake sharhi kan wannan sabon yunkurin, Aliko El-Rashid Haroun, wani tsohon jami'in leken asirin sojoji, ya gargadi dakarun na Najeriya da su yi la'akari da makwabciyar jihar Bornon, wato arewacin jihar Yobe, musamman tsakanin Yoben da Jamhuriyar Nijar. Ya ce idan aka lura, yankin ne mutanen Mamman Nur suke.
Wannan sabon farmakin Manjo Janar Abba Dikko ne zai jagorance shi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum