Yanzu an shiga wata na hudu da hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar Najeriya da koma wa kacokan ta hanyar teku.
Hukumar kwastam mai yaki da fasa- kwauri ta ce ba wai kawai raya tasoshin teku da kubucewar kudi zuwa kasar Cotonou ba ce ribar, matakin ya taimaka wajen dakile shigo da makamai.
Shugaban hukumar ta kwastan Hameed Ali ya ce ya kan kama makamai a motocin da ake shigo da su ta kan iyakokin kasa, kuma sau tari ba'a shigo da motocin ta sahihiyar hanya. Don haka matakin ya dakile fasa-kwaurin.
Koda yake hukumar ba ta fadi riba ko yawan kudin da matakin ya jawowa Najeriya ba, amma ta ci gaba da cewa duk da kokarin jami'ai sai an samu masu keta matakin tsaro.
Baya ga man fetur da ya fi samarwa kasar kudin shiga, hukumar kwastam ce mai samar da kudaden shiga masu yawa ga Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin jin yadda masana tattalin arziki ke cewa dangane da wannan lamari.
Facebook Forum