Yace duk inda basu amince da juna ba su gayawa junansu gaskiya domin ya zama wajibi su yi aiki tare, inji Ahmed Lawan.
Hakkin Majalisa ne ta taimaka ta hada kan 'yan majalisar har ma ta samu ta taimakawa shugaban kasa da kuma kwamitin zartaswa.
Dangane da cewa shi Sanata Ahmed Lawan yana kusa da shugaban kasa lokacin da ya zama shugaban masu rinjaye amma sai gashi bukata ta taso daga fadar shugaban kasan amma bata samu wucewa ba a majalisar, sai yace batun dimokradiya ke nan.
Sanata Ahmed Lawan yana mai cewa domin yana shugaban masu rinjaye a majalisa ra'ayinsa shi kadai ba zai sa duk abun da fadar shugaban kasa ke so zata samu ba. Amma yace aikinsa ne ya dinga tallar manufofin shugaba da gwamnatinsa ta bin sanatoci yana yi masu bayanin anfanin da kasar zata samu game da abun da bangaren shugaban kasa ke bukata.
Yace dimokradiya ta gaji a rasa samun wasu abubuwa amma ta hanyar tuntubar juna ana iya takaita koma baya. Yace da Shugaba Buhari ya hango matsalar kwamiti na musamman ya kafa. Yace su ma nan gaba zasu kafa nasu kwamitin domin a dinga tuntubar juna.
Akan batun Magu da Hamidu Ali na Kwastan da kwamishanonin zabe , Ahmed Lawan yace ana nan ana kokarin lalubo bakin zaren.
Ga rahoton Mahmud Kwari da karin bayani.
Facebook Forum