A wata sanarwa da hukumar ta rabawa manema labarai a Legas ta bayyana cewa an kama makaman ne tun kafin a fitar da sundukin waje.
A cewar kwamandan kwastan din mai kula da kudu maso yammacin kasar Monday Aboki yace an shigo da sundukin ne daga kasar Turkiya yayinda makaman an kerasu ne a kasar Italiya ko Amurka.
Kanar Aminu Isa Kontagora yayi tsokaci akan mahimmancin kama makaman musamman ta dalilin tsaro da zaman lafiyar kasar. Yace duk wand ya shigo da makamai idan dai ba hukuma ba to lallai yana da wata manufa wadda ba ta alheri ba ce. Abun alfahari ne cewa an kama makaman, injishi.
Wasu 'yan kasa ma sun tofa albarkacin bakinsu akan lamarin. Wani lamami yace sun ji dadi kuma suna farin ciki Allah ya sa hukumar kwastan tayi kokari ta kama makaman. Yace hukumar tana kokari wajen aiwatar da binciken kwakwaf ta tabbatar da abun da aka shigo dashi kasar.
Yanzu dai ita hukumar tana kan binciken gano wadanda suka shigo da makaman.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum