Amma ba a wurin taron ne bam din ya tashi ba kuma tuni jami'an tsaro suka samu nasarar cafke Ahmad Khan Rahami wanda ya aikata danyen aikin.
Kodayake mutane sun jikata sanadiyar bam din amma babu wanda ya rasa ransa kuma wasu ma cikinsu har sun fara murmurewa. Shi ma Ahmad Rahami yana asibiti saboda rauni da ya samu yayinda yake fafatawa da jami'an tsaro.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ko FBI da wasu jami'an tsaro sun yiwa manema labarai karin haske a taron da suka kira domin fadakar da jama'a. Sun bayyana abun da suka yi da kuma su keyi domin tantance dalilin aikata wannan aika-aikar. Sun ce zasu gano duk wadanda suke da nasaba da tashin bam din.
Magajin birnin New York B. Bilassio na cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron. Yace komi na hannun 'yansanda wadanda suke bincike kuma zasu hada kai dasu domin gano gaskiyar lamarin da zummar kare birnin daga hannun 'yan ta'ada.
Kwamishanan 'yansandan birnin yace ba zasu yi kasa a gwuiwa ba wajen binciken. Ya kira jama'a da su taimaka wajen tabbatar da tsaro. Yace da zara ka ga abun da baka yadda dashi ba ka shaidawa jami'an tsaro domin kada a cuci jama'a. Yace suna cigaba da binciken wanda suka kama.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.