A New York, wani kara mai karfin gaske ya girgiza unguwar da ake kira Chelsea dake yankin Manhattan, a daren jiya Asabar, abunda mahukuntan birnin na New York suka kira "da gangan aka kai aikata hakan" har mutane 29 suka jikkata.
Magajin garin birnin New York Bill DeBlassio ya ce "fashewar data auku a harabar adireshin 131 a layi na 23 da gangan aka yi shi, ya fadi haka ne lokacinda yake magana da manema labarai kusa da inda fashewar ta auku. Sai dai magajin gari DeBlassio, ya jaddada cewa, babu tabbacin wasu sanannun 'yan ta'adda ne suka haddasa fashewar.
Yace rundunar 'Yansanda da ma wasu hukumomin tsaro basu da wata masaniya dangane da wata barazana ta'addanci kan birnin mafi yawan jama'a a Amurka. Tuni shugabannin duniya suka fara isowa birnin gabannin bude taro babban zauren MDD na shekara shekara.
Ba nesa daga inda wannan fashewa ta auku, hukumomin birnin sun gano wata nakiyar wacce bata tashi ba akan titi mai lamba 27. An dana su ne cikin tukunyar nan da ake kira "Pressure Cooker," aka hada da woyar celula, aka saka cikin wata ledar shefene.