Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sakkwato Tace Za Ta Binciki Harin Jirgin Sojoji Da Ya Kashe Mutane 10


Harin Jihar Sakkwato
Harin Jihar Sakkwato

Gwamnatin jihar Sakkwato tace za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen bincikar musabbabin harin da jirgin saman yakin Soja ya kai kan wasu al'ummomin jihar wanda ya yi sanadin salwantar rayukan mutane goma.

Harin ya faru ne lokacin da jirgen yakin ke kai hare-hare akan sansanonin 'yan ta'addar Lakurawa da ke barazana ga zaman lafiyar yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu ya tabbatar da irin hasarar rayuka sanadiyar harin da jirgin yakin soja a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Silame. Gwamnan yace an kai harin ne bisa kuskure.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake samun kuskuren jirgin yaki ya kai farmaki akan jama'ar gari, kamar yadda ya taba faruwa a watan Disamba 2023 a Tudun biri dake jihar Kaduna, da kuma jihohin Nasarawa da Adamawa.

'Yan Najeriya suna ci gaba da kokawa kamar yadda kungiyar tuntuba ta arewa ta ce ya kamata a ce an kai matakin da za'a daina yin irin wannan kuskure.

Jami’in kula da yada labarai na rundunar soji mai aikin samar da zaman lafiya na fansar yamma, Lt. Col Abubakar Abdullahi yace, rundunar sojin tana aikin ne bisa bayanan siri da take samu.

Rundunar sojin ta nuna rashin jin dadi kan yadda wasu kafafen sadarwa ke yayata labaran da basu da tabbas, kamar yadda Lt. Col. A Abdullahi ya ce.

Yanzu jama'ar wadannan garuruwan na Gidan sama da Rumtuwa na ci gaba da alhinin rashin mutane goma da kuma zaman dar-dar kan abinda ka iya sake faruwa.

Saurari cikakken rahoton:

Gwamnatin Sakkwato Tace Za Ta Binciki Harin Jirgin Sojoji Da Ya Kashe Mutane 10
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG