Wannan kuskuren ya faru a gundumar Gereshk, inda ake wani kazamin fada tsakanin 'yan tsageran Taliban da sojojin gwamnati, inda Amurka ta kashe sojojin gwamnatin Afghanistan 15.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Afghnistan Dawlat Waziri ya ce a yayin fadan, wani kamami mai lizami da jirgin Amurka mara matuki ya harbo ya fada kan wani wurin binciken ababen hawa na sojojin gwamnati da daren jiya Jumma'a. Ya gaya ma Muryar Amurka cewa wannan hari ya yi sanadin mutuwar sojoji akalla 15 da kuma raunata wani guda.
Kwamandojin sojin Amurka sun tabbatar cewa an kashe wasu jami'an tsaro 'yan Afghanistan da ke aiki tare da sojojin gwamnati Afghanistan. Jami'an sojin na Amurka sun fitar da takardar bayani mai bayyana al'amarin da "abin takaici" sannan su ka yi alkawarin gudanar da bincike don sanin musabbabin faruwan al'amarin.
Facebook Forum