Wasu mutane na hannun daman shugaban kasar Amurka Donald Trump sun fara binciken mukarabban babban jami’in gudanarda bincike mai zaman kansa na musamman Robert Mueller, da zummar gano wasu aiyukkan assha da su mukarabban nashi watakila suka aikata da zasu nuna rashin cancantarsu da taka rawa a binciken da ake mai alaka da Rasha da shi Trump din, a cewar wasu rahotanni da suka fito a daren jiya Alhamis.
Daya daga cikin lauyoyin shugaba Trump, Jay Sekulow, yace lauyoyin shugaban “suna duba duk hanyoyin da wadanan mukarabban ke da wani abinda zai saka ayar tambaya a ikin nasu, kuma zasu rinka nuna hakan a duk wata dama da ta samu, ciki harda tinkarar shi kansa Robert Muller kan zancen.
Shugaba Trump ya nemi jin ta bakin masu bashi shawara kan cewa ko zai iya amfani da ikonsa wajen yin ahuwa akan ‘yan hannun damarsa da iyalansa har ma da shi kansa daga binciken da ake na alarsu da Rasha.
Jaridar Washington Post ta fitar da rahoto inda ta ruwaito hirar da tayi da wani dake da masaniya game da batun.
Wani mutum na biyu kuma ya fadawa jaridar cewa lauyoyin Trump sun jima suna tattaunawa a tsakanin su-ya-su akan batun ahuwar.
A cewar jaridar New York Times, ‘yan hannun damar shugaban na neman duk wasu hanyoyi da zasu kawo batanci ga masu binciken.
Facebook Forum