Mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan harkar tsaro ya ce mummunan tashin hankalin nan da ya auku a wurin gangamin masu da'awar fifita farar fata a Charlottesville, jihar Virginia, ya cimma abin da za a kira "ta'addanci."
A wata hira da gidan talabijin na ABC, H.R. McMaster ya bayyana abkawa da mota da aka yi cikin cuncurundon masu zanga-zangar kishiyar dayar a ranar Asabar inda har aka kashe Heather Heyer 'yar shekaru 32 da haihuwa a matsayin abin da ya kira, "wani mummunan laifi wanda mai yiwu wa tsana ce ta janyo shi."
Haka zalika, wasu mutane 19 kuma sun samu raunuka, sannan wasu 'yan sandan jihar ta Virginia, wadanda ke sa ido kan gangamin daga ta sama sun mutu a wani hadarin jirgin samansu.
Jiya Lahadi, Fadar Shugaban Amurka ta White House ta kare matsayin Shugaba Trump game da wannan mummunan tashin hankalin da ya auku a Virginia, saboda sukar sa da aka yi na cewa bai fito fili ya yi Allah wadai da masu tsattsauran ra'ayin fifita farar fatan ba.
A halin da ake ciki kuma, Gwamnan jihar Virginia Terry McAulliffe, ya sa an yi dan tsit a yayin wata addu'ar da aka yi ma marigayiya Heather Heyer a jiya Lahadi a Charlottesville wadda ta mutu a lokacin da mai motar ya abka cikin jama'a.
Facebook Forum