Wata cibiyar kare hakkin bil adama mai sa ido a Siriyya ta fada yau Laraba cewa hari ta sama da ake kyautata zaton hadakar dakarun da Amurka ke jagoranta suka kai shi, ya kashe akalla mutane talatin da uku a wata makaranta kusa da birnin Raqqa.
Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Observatory ta fadi cewa harin ya auku ne da safiyar jiya Talata a wajen kauyen al-Mansoura, kuma wannan makarantar ana amfani da ita wajen sauke ‘yan gudun hijirar da rikicin Siriyya ya raba da gidajensu.
Birnin Raqqa dai shine shelkwatar ‘yan kungiyar ISIS, kuma kwato garin shine babban burin yawancin dakarun dake yaki da mayakan na ISIS.
Gamayyar dakarun kasashen da Amurka ke jagoranta, da suka kai kusan 12 dake kai hare-haren akan ‘yan ISIS a Siriyya, sun yi ta auna birnin na Raqqa cikin ‘yan kwanakin nan, kuma rahotannin dakarun ya nuna cewa, tsakanin ranakkun Asabar, Lahadi da shekaranjiya litinin, an kai hare-hare kusan ashirin-ashirin a kowace rana.
Facebook Forum