Babbar jam’iyar hamayya a Demokaradiyar jamhuriyar Congo ta bayyana Jean Pierre-Bemba wanda kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa take tuhuma da aikata laifukan yaki a matsayin dan takarar shugaban kasarta. Jam’iyar Movement for the Liberation of Congo ta sanar da tsaida wannan shawarar ne jiya asabar. Bemba, tsohon mataimakin shugaban kasar Congo ta Kinshasa, yana kulle a gidan yarin kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa, wadda take tuhumarshi da aikata laifukan yaki uku da kuma laifukan gallazawa bil’adama biyu. Ana zarginshi da jagorantar kungiyar mayakan da ta kashe daruruwan mutane da kuma yi masu fyade a jamhuriyar dake tsakiyar Afrika cikin shekara ta dubu biyu da biyu, da dubu biyu da uku. Ya musanta aikata wadannan laifukan. Bemba yazo na biyu a zaben shugaban kasar congo ta Kinshasa da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da shida da shugaban kasar mai ci yanzu Joseph Kabila ya lashe. Shugaban kasar ya sake tsayawa takara a zaben da za a gudanar cikin watan Nuwamba bana.