An kashe madugun ‘yan tawayen kasar Sudan yau asabar ‘yan kwanaki bayan amincewa da daina musayar wuta a yankin. Rundunar sojin Sudan ta Kudu da wata majiya ‘yan tawayen tace an harbe aka kashe Gatluak Gai. Gai yasa hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta da sabuwar gwamnatin Sudan ta Kudu makon da ya gabata. Akwai sababin rahotanni kan wanda ke da alhakin kashe shi, inda wadansu ke cewa, sojojin Gai ne suka kashe shi, yayinda wadansu ke cewa, sojojin Sudan ta kudu-SPLA ne suka kashe shi. Gai ya jagoranci daya daga cikin kungiyoyin mayaka da dama a sabuwar kasar ta duniya Sudan ta Kudu. A cikin jawabinshi na neman zaman lafiya, shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir ya sanar da yiwa mayakan da suka yaki gwamnatin kasar kwanan nan ahuwa.
An kashe madugun ‘yan tawayen kasar Sudan yau asabar ‘yan kwanaki bayan amincewa da daina musayar wuta a yankin.