Har yanzu dai akwai alamun bukatar kara wayar da kan al'umma game da guje wa cunkoso don dakile yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, saboda duk da dokar hana zirga-zirga mutane na ci gaba da taruwa a wuri guda.
Filayen wasan kwallon kafa da kuma majalisun hira na unguwanni a Najeriya na ci gaba da tara mutane saboda yadda magidanta suka fara gajiya da zaman cikin gida, abun da ke kara fargabar yada cutar ta coronavirus a tsakanin al'umma.
Gwamnatin jihar Kaduna na cikin jihohin da suka fara kafa dokar hana zirga-zirga da zaman gida amma ta ce har yanzu akwai matsala game da bin wannan doka, inji kwamishinan tsaro da al'amurran cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Aruwan ya ce an haramta taron mutane da waya, ciki har da taron kallon wasan kwallon kafa a unguwanni ko a inda ake buga tamaula, amma abin takaici shine wasu sun ki bin wannan dokar, a cewarsa.
Manazarta al'amurran yau da kullun na ganin wajibi ne gwamnati ta tsaurara matakan hana cunkoson jama'a don magance yaduwar wannan cuta.
Barista Ahmadu Sani Sada, lauya ne mai-zaman kansa a jihar Kaduna, ya ce har yanzu ba a daina cunkoso a wajen taron kallon wasan kwallon kafa ko kuma zuwa gidajen kallo ba. Baristan ya kuma ce ya kamata hukumomi su tsaurara dokar hana cunkoso tare da kara fadakar da al’umma.
Daya daga cikin 'yan wasan kwallon kafa, kuma mai horarwa, Hamisu Okocha ya ce fita wasan kwallon na taimakawa wajen motsa jiki masamman a wannan lokaci na zaman gida.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Isah Lawal Ikara.
Facebook Forum