A karon farko, an samu mutum fiye da 100 da ke dauke da cutar Coronavirus cikin yini daya a Najeriya.
Hakan ya nuna cewa adadin masu Coronavirus sai dada karuwa yake yi a kasar yayin da yanzu mutum 782 ne ke fama da wannan cutar.
Hukumar dakile cututtuka ta NCDC ce ta bayyana cewa mutum 117 sun sake kamuwa da cutar a cikin alkaluman da ta fitar na baya-bayan nan.
Cikin sabbin mutanen da suka kamu da cutar akwai mutum 59 daga jihar Legas, 29 a birnin Abuja da kuma 14 a Kano.
A cikin mutum 782 da ke dauke da cutar a kasar, har yanzu Legas ce ke kan gaba da mutum 430 sai kuma Abuja da mutum 118.
Tun bayan da NCDC ta fitar da wadannan sabbin alkaluman, hankulan mutane ya tashi, musamman ma a shafukan sada zumunta kasancewar ba a taba samun mutane da yawa da suka kamu da cutar cikin yini guda ba kamar yanzu.
Facebook Forum