Bayan warkewar Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, gwamnatinsa ta yi ittikafin kara mayar da hankali wajen yaki da cutar.
A ranar Laraba ne gwamnan ya bayyana sakamakon warkewa daga kamuwa da cutar, bayan gwaje-gwaje biyu a jere da su ka tabbatar da warkewar shi.
Ya ce “a ranar Litinin mu ka sami bakin labarin sake kamuwar mutum uku a wannan jihar, za su samu cikakkiyar kulawa daga jami'an lafiyar Kaduna kuma muna yi musu fatan warkewa daga cutar Corona cikin sauri.”
“A matsayina na wanda ya ji yadda ake ji da wannan cutar, ba zan yi fatan ta kama koda mafi tsananin abokin gaba na ba,” a cewar gwamnan.
Kwamishinan tsaro da al'amurran cikin gida na jihar ta Kaduna, malam Samuel Aruwan ya ce yanzu ne ma za a kara zafafa yaki da wannan cutar ta Coronavirus.
Kafin gwamnan ya karkare jawabinsa, ya bayyana cewa gwamnatinsa zata samar da takunkumin rufe hanci da baki kyauta ga marasa karfi.
Ya zuwa yanzu dai mutum 9 ne suka kamu da cutar ta Coronavirus a jihar.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum