Gwamnonin Jihohin Najeriya 36 sun yi taro a karo na 6 ta yanar gizo tun bayan bullar cutar Coronavirus, inda suka amince da kaddamar da dokar kulle kasar baki daya har na tsawon makonni biyu domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.
Kakakin Kungiyar Abdulrazak Bello Barkindo ya bayyana wa Muryar Amurka cewa cewa sun saurari bayanai daga Gwamnonin Kano da Legas da Bauchi da Oyo da kuma jihar Ogun kan darrusan da suka koya daga yaki da cutar covid 19.
A cewarsa an zabi wasu gwamnoni 6 da kuma shugabannin kungiyar wadanda za su gana da mataimakin shugaban Kasar Najeriya domin bayyana masa irin matsalolin da jihohi ke fuskanta.
Ya ce, “gwamnonin ne suka bayar da shawarar rufe iyakokokin dukkannin jihohi da kuma birane domin yawancin inda ake samun bullar cutar, wasu ne ke kawo ta daga wata jihar.”
“Yanzu haka jihohi 25 ne ke da cutar, idan aka bar mutane su ci gaba da yawo, sai kowacce jihar ta sami cutar.”
Barkindo ya kuma bayyana mana cewa masu sufurin kayan abinci da na masarufi ne kawai za a bari su yi zirga-zirga.
A bangaren tallafi kuma Barkindo ya ce saboda korafe-korafen da ake ta yi na cewa ana bayar da kayan tallafi amma baya isa ga masu bukata, gwamnonin sun bayar da shawarar bai wa mutanen da kawai ke bukatar tallafin, kamar marasa karfi da kuma tsofaffi.
Wannan matakin da gwamnonin suka dauka yana daya daga cikin matakan takaita yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus wacce mutum 873 ke fama da ita a kasar.
Facebook Forum