Ministan muhalli a Najeriya Amina Muhammad ta bayyana hakan a taron koli karo na goma da aka gudanar a garin Lafiya, fadar jihar Nasarawa. A jawabinta, ministan muhallin ta kara jaddada kudurorin wannan gwamnati da suka hada da farfado da tattalin arziki, da inganta tsaro da kuma karfafa manufofin gudanar da mulki.
Ministan ta bayyana cewa ma’aikatar kula da muhalli ta dukufa wajan tsare hamada ta hanyar dashen itatuwa, fadada shirin hana zaizayewar kasa a jihohi goma sha tara, tsaftace yankin Ogni da dakatar da fitar da katakai zuwa kasashen waje da saurn su.
Amina Muhammada a jawabinta ta ce suna so su kare muhalli, da kuma kirkiro ayyukan yi ta amfani da kayan bola da samar da makamashi.
A hirar su da wakiliyar sahen Hausa na muryar Amurka Zainab Babaji, Karamin ministan muhalli ya ce babban makasudin taron da aka gudanar a jihar Nasarawa shine domin tara dukkan kwamishinoni dake kula da harkokin kare muhalli a duka jihohin dake tarayyar Najeriya da babban birnin tarayya domin suzo su tattauna matsalolin da ke damun su. Idan an yi rin wannan taro aka hada dukkan matsalolin, sai a je dasu majalisar koli ta tarayyar Najeriya inda ministoci da shugaban kasa ke zama domin zartar da hukunci.
Shi kuma gwamnan jihar Ummaru Tanko Al’makura ya bayyana cewa jihar Nasarawa na daya daga cikin jihohin da ke fama da ambaliyar ruwa da zaizayewar kasa, dan haka wannan taro da aka gudanar a jihar ya ba jihar damar samun shiga cikin jerin sunayen jihohin da za’a mikawa majalisar dinkin duniya domin taimaka masu wajan shawo kan lamarin.
Zainab Babaji.