Hukumar da gwamnatin ta kafa ta kumshi ma'aikatu guda ukku ko hudu da suka hada da ma'aikatar muhalli da ma'aikatar filaye da ma'aikatar ayyuka da jami'an 'yansanda da dogarawan tsaron farar hula ko Civil Defence.
Chief Ishola Adisa kwamishanan muhalli na jihar yace aikin wannan hukumar shi ne ta kama duk wanda ya karya dokokin muhalli a jihar. An kuma kafa kotun muhalli na mausamman da zai saurari kararraki dake da alaka da karya dokokin muhalli a kuma hukumtashi nan take.
Gwamnatin ta dauki matakan ne domin ilimantar da al'ummarta domin su kaucewa cunkushewa hanyoyin ruwa domin hana aukuwar ambaliyan ruwa a duk fadin jihar.
A shekarar 2011 aka yi wata munmunar ambaliyar ruwa a jihar da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama., da lalata gidaje da makarantu da asibitoci da hanyoyi da gadoji da dai sauransu.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.