Taron na yin nazari da tsokaci ne akan matsaloli da nasarorin da tattalin arzikin kasashen Afirka ke fuskanta da zummar tsara hikimomin da za'a bi nan gaba.
Shugaba Muhammad Buhari ya kira gwamnonin da su fito da wani tsarin da zai warware mataslolin da kasashen Afirka ke fuskanta yanzu musamman idan suka yi la'akari da cewa kasashen dake da man fetur suna fuskantar babban kalubale.
Shugaban ya cigaba da cewa matsalolin da kasashen dake da mai suke fuskanta sun bazu zuwa sauran kasashen wadanda dama can suna fama da nasu matsalolin tattalin arzikin. Duniya gaba daya tana fuskantar matasalar tattalin arziki ganin yadda harkokin cinikayya da muamalar cudanya suka yi kasa.
Dr. Obadiah Mailafiya tsohon mataimakin gwamnan bankin Najeriya yace taron nada mahimmanci a daidai wannan lokacin domin su gwamnonin sukan hadu kowace shekara su tattauna akan irin matakan da zasu dauka na jagoran tattalin arzikin kasashensu.
Yace a wannan shekarar an fuskanci matsaloli iri-iri saboda haka taron zai tainmaka masu akan shawara da juna dangane da matsalolin.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.